Babban bankin Najeriya CBN ya ce kawo yanzu ya saki kudi masu yawan gaske ga Bankunan kasuwanci a kasar
A cewar bankin ya saki kudin ne ga Bankunan, domin su samu damar baiwa al’umma da suke tsananin bukatar kudin a hannu yanzu haka.
CBN ya ce daga ranar Alhamis ya fara sakin biliyoyin kudin ga Bankunan kasar, domin dai su sanya su a naurar cirar kudi ta ATM da nufin al’umma su samu. Punch ta rawaito.
KU KARANTA: A Gaggauta Tsige Jami’in Tattara Sakamakon Zaben Jihar Kebbi – APC ta Fadawa INEC
Daga bisani ne kuma bankin ya bayar da umarnin bankuna su bude a karshen mako, domin dai baiwa al’umma dama su je domin samun kudin da zasu biya bukatun su.
Da alama kuma wannan umarni ya taimaka wajen saukakawa al’umma, domin kuwa a zagayen da DIMOKURAƊIYYA ta gudanar a wasu tituna na jihar Kano ta iske yadda Bankunan suka bude suna baiwa abokan hulɗar su damar shiga domin biya musu bukatun su.
Yawancin Bankunan dake kan titin zuwa Zariya a jihar Kano sun bude a karshen mako.
A wani labarin kuma: Zaben Gwamna: ‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutane 79 Da Ake Zargi Da Karya Doka A Sokoto
Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto a ranar Lahadin da ta gabata ta ce jami’an tsaro sun kama mutane 79 da ake zargi da hannu a wasu laifuka a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Wata sanarwa da DSP Sanusi Abubakar, kakakin rundunar ‘yan sandan ya raba wa manema labarai a Sokoto, ta ce wadanda aka kama mutane ne da suka saba wa dokar takaita zirga-zirga da kuma wasu laifuka da suka saba wa dokar zabe.