Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana cewa masu kada kuri’a a zaben 2023 wadanda ka yiwa rajistar zabe akwai mata guda miliyan 44,414,846, yayin da maza kuma suka kasance guda miliyan 49,054,162 ne.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da shugabannin jam’iyyun siyasa a hedikwatar hukumar da ke Abuja ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Da PDP Ta Shigar Kan Gwamnan Kwara Bisa Mallakar Jabun Takardu
Yakubu, a yayin taron, ya gabatar da rajistar masu kada kuri’a na 2023 ga shugabannin jam’iyyun siyasa 18 gabanin zabe kamar yadda dokar zabe ta 2022 ta bukata.
Hukumar ta gabatar da rajista mai dauke da mutane miliyan 93,469,008 domin kada kuri’a a babban zaben shekarar 2023.
Daga cikin wadanda suka yi rajistar zabe, adadin matasa masu shekaru 18 zuwa 34 ya kai miliyan 37,060,399, wanda ke wakiltar kashi 39.65% na daukacin wadanda suka yi rajista, yayin da tsofaffi masu shekaru 50 zuwa 69 suka kai miliyan 17,700,270, wanda ke wakiltar kashi 18.94% na adadin wadanda suka yi rajista.
A halin da ake ciki, hukumar ta yi watsi da rade-radin dage zaben 2023.
Hukumar ta jaddada kudirinta na gudanar da babban zabe mai zuwa kamar yadda aka tsara.
Yakubu ya ce hukumar ba ta tunanin dage babban zaben kasar a watan Fabrairu da Maris na wannan shekara.
Ya ce, “Hukumar ba ta tunanin wani gyara ga jadawalin zabe balle a dage babban zaben. Tabbacin da hukumomin tsaro suka yi na tabbatar da isassun kariya ga ma’aikata da tsarin yana kara karfafa aniyarmu na ci gaba.
“Zaben 2023 zai gudana kamar yadda aka tsara. Duk wani rahoto da za a kai wa kasar ba matsayin hukuma ba ne,” inji shi.
A wani labarin kuma, Dubu Ta Cika: An Kama Kwamishinan Yan Sandan Bogi da Ya Damfari Wani Miliyan N250m
Hukumar binciken manyan laifuka ta jihar Legas, ta kama Oluwole Akande, dan shekara 55, bisa zarginsa da laifin yin sojan gona wajen kwaikwayon kwamishiniyar ‘yar sanda, CP Yetunde Longe, da kuma damfarar wani tsoho mai shekaru 80 naira miliyan 250.
Kwamishiniyar hukumar kula da layin dogo, CP Yetunde Longe, ta tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya kamun ranar Laraba a Legas.