Malaman jihar Kaduna sun goyi bayan matakin da Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya dauka na hana sallar Idi a jihar.
Gwamnan ya dauki matakin ne yayin wata hira da ya yi da ‘yan jarida ranar Talata wadda aka yada kai tsaye a gidajen rediyon jihar da kuma wasu kafofin sada zumunta.
A cewar gwamnan, ya dauki matakin ne domin dakile yaduwar cutar korona wadda ta addabi kasashen duniya.
A hirarsa da gidan Rediyon BBC Hausa, daya daga cikin malaman addinin musulunci a jihar, Malam Tukur Adam Al-Manar, ya ce sun amince da gwamnan ne bayan taron da ya yi da su.
Malamin ya bayyana cewa tun da farko malaman sun je wurin gwamnan ne da niyyar a sassauta dokar domin bayar da dama a ci gaba da gudanar da sallar Juma’a da kasuwanci.
Amma daga baya da gwamnan ya yi musu bayani tare da wasu kwararrun likitoci kan illolin yin hakan, sai suka gane hukuncin da gwamnan ya yanke “akwai maslaha ga al’umma”, in ji Malam Tukur.
“An gamsu a wurin kan cewa lallai matakan da ya dauka su ne suka fi wurin kare rayuka.”
“Saboda ya nuna cewa an yi wata biyu kenan mutane kulle a gidaje, ana daf da abin ya wartsake kuma a ce an birkita abin, wata biyun da aka yi sun zama sun tafi a banza kenan,” in ji Malam Tukur
Malamin ya bayyana cewa malamai daga bangaren Izala da Dariƙa da Fityanu da sauran bangarori sun halarci wannan tattaunawa kuma sun gamsu da hujjojin da gwamnan ya bayar.
Tun a baya dai, gwamnan ya soki wasu malamai waɗanda ya zarge su da yi masa gazafi inda ya yi masu ‘Allah-Ya-isa’.
A cewarsa “Ko a Makka ba za a yi sallar Idi ba, amma mu a nan malamai sun hau mumbari suna cewa mun hana sallah. Kuma sun sani. Saboda haka Allah ya isa. Na yafe wa duk wanda ya zage ni, amma ba zan yafe wa wanda ya yi min kazafi ba.”