Daga: Abbas Yakubu Yaura
Kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ta roki hukumar shirya jarabawar ta kasa NECO da ta canza ranar jarrabawar ta a watan Yulin shekarar 2022 sakamakon karon da ta yi da ranar farko ta babbar sallar Eid-el-Adha.
Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya yi wannan roko a ranar Lahadi a wata sanarwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/gwamna-ganduje-ya-amince-da-sakin-naira-miliyan-33-ga-daliban-jihar-dake-karatu-a-faransa/
“Muna da cikakkiyar masaniyar cewa lamarin yaci karo ba da gangan ba ne domin a zahiri NECO ta nuna farin cikinta ta hanyar ware mako guda domin gudanar da bukukuwan Sallah (Litinin, 11 ga watan Yuli zuwa Juma’a 15 ga Yuli) kuma hakan ya bayyana a cikin jadawalin ta.
“Don haka muna kira ga mahukuntan NECO da su mayar da jarrabawar wannan rana ta (Asabar 9 ga watan Yuli, 2022 kadai) zuwa wata rana ta daban domin baiwa dalibai Musulmi da suka ci karo da zana jarabawar a ranar sallah dama.
“Za a iya daukar takardar wadda tun farko aka sanya ranar Sallah a ranar Alhamis 14 ga watan Yuli, 2022 wanda yana daya daga cikin ranakun da NECO ta kebe domin hutun Sallah.”
A Wani Labarin Kuma Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin sakin kudi Naira miliyan 33, a matsayin alawus ga daliban jihar, wadanda ke karatun digirin farko a jami’o’i daban daban dake ƙasar Faransa.
Kwamishinar ilimi mai zurfi ta jihar Kano Dakta Mariya Mahmoud Bunkure ce ya bayyana hakan, a cikin wata Sanarwa da aka rabawa manema labarai yau Lahadi.
Mariya ta kara da cewa wannan kason wani bangare na tallafin da gwamnatin Kano, ta kuduri aniyar aiwatar ga daliban Kano dake karatu a Faransa, karkashin wani shirin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Kano da kasar Faransa.
Wannan tallafin dai an bayar da shi ne ga daliban, wadanda suke karatun kimiyya da fasaha, a can ƙasar, da nufin idan sun kammala sun dawo, jihar Kano tayi alfahari da su.
Sanarwar ta kara da cewa karkashin wannan shiri, malamai da dama a manyan makarantun gaba da sikandire a jihar sun Amfana, da samun digiri na biyu, da kuma na uku.
Kazalika wasu daga cikin tuni sun kammala sun dawo jihar Kano, yayin da wasu ke a shekarar karshe don kammalawa, kuma suma zasu dawo jihar Kano, don ci gaba da tallafawa bunƙasar jihar.