Shugaban ƙasar Cuba, Muguel Diaz-Canel da takwaran sa na ƙasar Nicaragua, Daniel Ortega, sun taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasan Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bisa nasarar da ya samu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023. Rahoton Vanguard
Wata sanarwa da hadimin Tinubu kan harkokin watsa labarai, Tunde Rahman, ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana saƙonnin taya murnar shugabannin ƙasashen biyu ya iso ne a wasiƙu daban-daban.
KU KARANTA KUMA: Budurwar Cristiano Ronaldo ta bayyana wani sirri dangane da rayuwar su ita da ɗan wasan
Rahman ya ambato shugaban ƙasar Cuba na bayyana nasarar Tinubu a matsayin “sake jaddada kuɗirin cigaba da ƙarfafa ɗaɗaɗɗiyar dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu.”
A ɓangaren Nicaragua kuwa, saƙon su wanda Ortega da mataimakin sa Rosario Murillo, suka rattaɓawa hannu, sun yi Najeriya fatan alheri.
“Muna turo da fatan samun zaman lafiga da cigaban Najeriya, a yayin da muke sake jaddada alƙawarin mu na cigaba da ƙarfafa alaƙar mu mai ƙarfi wacce ta haɗa kan mutanen mu da gwamnatocin mu.” A cewar su
APC Ta Zargi INEC Da Rike Bayanan Da Ake Bukata Don Shigar Da Kara Kotu
Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben da aka kammala a jihar Ribas, Patrick Tonye-Cole ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta INEC da jinkirta fitar da wasu takardu da ake bukata domin shari’arsu a kotun.
Tonye-Cole, yayin wata zanga-zangar da aka yi a babban ofishin hukumar ta INEC na jihar a ranar Juma’a a Fatakwal, ya nuna damuwarsa kan yadda alkalan zaben suka ki sakin takardun da aka yi amfani da su a zaben da ya gabata domin su ci gaba da shari’arsu a kotun