By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane 10 ne ake fargabar sun mutu a yayin da wani ginin cocin, ma’aikatar Salvation, da ke unguwar Okpanam a karamar hukumar Oshimili ta Arewa a jihar Delta ya ruguje a yammacin ranar Talata.
Wasu shaidu sun ce wadanda ba a tantance adadinsu ba sun makale a karkashin tarkacen ginin da ya ruguje.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa ginin da aka fara amfani da shi a karon farko ya ruguje ne da misalin karfe 5.55 na yamma a lokacin da ake tsaka da gudanar da hidimar a yammacin ranar Talata.
Kimanin mutane takwas ne aka ce an ceto ba tare da jikkata ba a ginin da ya ruguje yayin da wasu hudu da suka samu raunuka daban-daban aka garzaya da su zuwa Asibitin kwararru na Asaba domin kula da lafiyarsu.
An ga masu ibada da ‘yan uwa da masu tausayawa suna kuka a dai dai lokacin da ake kara zage damtse wajen ganin an ceto sauran wadanda rikicin ya rutsa da su.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, sakataren gwamnatin jihar, Cif Patrick Ukah; Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Ononye Mordi; tawagar jami’an kungiyar agaji ta Red Cross da kuma wasu ma’aikatan hukumar kashe gobara suna cikin aikin ceton.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, an kasa samun jin ta bakinsa kan rugujewar ginin cocin.