By Abbas Yakubu Yaura
Yusuf Abdullahi, Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi, yace akalla mutane 16 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a jihar ranar Lahadi.
Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira daya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Litinin a Bauchi.
A cewarsa, hatsarin ya rutsa da wata babbar mota da kuma wata motar kirar Toyota Hummer ta kasuwanci, a kauyen Bambal dake kan titin Kano zuwa Jama’are da karfe 7:00 na dare.
Kwamandan sashin, wanda yace sai da jami’an sa suka dauki kimanin mintuna bakwai kafin su isa wurin domin share wurin da lamarin ya faru,sannan ya danganta hatsarin da saurin gudu daya wuce kima.
“Mutane 16 ne hatsarin ya rutsa dasu da suka hada da maza 10 da mata shida kuma dukkan mutanen dake cikin motar sun rasa rayukansu a hadarin.
“ Motar Bas din Hummer ta Kama da wuta bayan ta bugi motar kuma babu wani rai daya tsira daga hatsarin.
Kazalika “ wasu mutanen sun kone ta yadda ba a iya gane su a cikin motar Hummer,” in ji Abdullahi.
Sannan ya bayyana cewa an ajiye gawarwakin ne a dakin ajiye gawa na babban asibitin Kiyawa dake hanyar Kano zuwa Jama’are domin tantancewa.
Kwamandan sashin ya shawarci masu ababen hawa dasu kasance masu sane da ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa a kodayaushe yayin da suke bin hanyoyin.