By Abbas Yakubu Yaura
Kungiyar likitocin Najeriya reshen jihar Kwara, ta yi kira da a sako mamban kungiyar, Dakta Zubair Erubu, wanda aka yi garkuwa da shi a daren ranar Alhamis a gidan gonarsa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban NMA, Farfesa Baba Issa ya fitar ranar Litinin a Ilorin; da Sakataren kungiyar, Dakta Tijani AbdulRasheed.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an sace Erubu ne a gidan gonarsa dake Ago-Oja a karamar hukumar Asa a ranar 9 ga watan Disamba.
“Erubu wanda ya kasabce yana aikin likitanci da himma kuma yawancin ayyukansa,yana yin sune musamman a asibitin Fadima mai zaman kansa.
Sannan ya kasance “Mai jin kai ne, wanda ke yi wa marasa galihu hidima a gidan gonarsa ba tare da samun komai ba.
“Erubu ya himmatu wajen taimaka wa talakawa da marasa galihu a cikin al’umma.
“Abin takaici ne a ce wanda ya sadaukar da rayuwarsa don taimakon wasu shi ne wanda a yanzu ‘yan fashin suke farauta tare da sace su da tsare su.
Shugabannin NMA sun kuma yi kira ga hukumomin tsaro dasu tabbatar da tsaron sauran likitocin da kwararrun likitocin dake aiki a jihar da ma Najeriya baki daya.
Kazalika “Ya kamata gwamnati ta samar da isassun matakai don kare wadanda suka yanke shawarar ci gaba da zama a kasar.