Mazauna garin Kubwa da ke karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja sun shiga cikin firgici bayan da wani bene mai hawa biyu ya ruguje wanda ya yi sanadin mutuwar mutum daya tare da barin ma’aikata da dama amakale.
Ginin wanda ake kan gina shi ya ruguje ne a titin Hamza Abdullahi dake kan titin Gado Nasco.
Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis da misalin karfe 11:30 na dare.
A lokacin da wakilin majjyar Dinokuradiyya ya ziyarci wurin a safiyar jiya, ya cimma jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA na gudanar da aikin ceto.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu Zai Raya Najeriya Kamar Yadda Ya Raya Legas Idan Yayi Nasara – Okiro
A cewar NEMA, mutane shida ne lamarin ya shafa.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Manzo Ezekiel ya fitar, ya ce an sanar da hukumar ta NEMA faruwar lamarin da misalin karfe 1:00 na safe, inda nan take ta tattara jami’anta domin kai daukin gaggawa, wadanda suka hada da hukumar bayar da agajin gaggawa ta Abuha, hukumar kashe gobara, jami’an tsaron farin kaya da kuma ‘yan sanda zuwa wurin.
Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Babban Birnin Tarayya Abuja (FEMA), Alhaji Abbas Idriss, ya sanar a jiya cewa mutane biyu da suka makale a ginin da ya ruguje a Kubwa da ke wajen birnin Abuja, sun mutu.
Alhaji Idriss ya ce aikin ceto a wurin da ya rufta ya zo karshe tare da ceto mutane biyar da ransu; uku sun samu raunuka daban-daban yayin da mutane biyu ba su samu raunuka ba.
A halin da ake ciki, karamar ministar babban birnin tarayya Abuja, Dakta Ramatu Tijjani Aliyu, ta jajantawa iyalan wadanda ginin Kubwa ya shafa.
Hafeez Olayinka, daya daga cikin wadanda aka ceto daga ginin da ya rufta, ya ce ya shafe sa’o’i a cikin ginin yayin da lamarin ya rutsa da shi..
Olayinka, wanda ya koma inda lamarin ya faru bayan ya yi masa jinya a asibiti, ya shaida wa manema labarai cewa ya isa ginin da ya ruguje ne a ranar Litinin.
“Ni da wasu mun makale tun daren Alhamis. Da misalin karfe 11:30 na dare ranar Alhamis, mun lura ginin yana rugujewa. Mun yi ƙoƙarin tserewa amma ba mu iya yin hakan ba. An ceto mu, Mh biyar a safiyar yau aka kai mu asibiti,” inji shi.
Uwargida Uba Gloria, wacce ke zaune a gefen ginin, ta ce ginin da ya ruguje tun da farko wani kantin sayar da kayayyaki ne amma kwanan nan ya koma gidajen zama.
Ta kara da cewa, wasu tubalan da aka yi wa ginin na iya haifar da rugujewar.
Wani masanin gine-ginen, Daniel Chuks, wanda shi ma mazaunin yankin ne, ya ce rashin kyakykyawan ayyuka a tsarin gine-gine kan haifar da gazawa ko rugujewa.
A WANI LABARIN KUMA: Hukumar NEMA Tayi Karin Haske Kan Ginin Abuja Daya Ruguje
An tabbatar da mutuwar mutane biyu da suka makale a karkashin baraguzan gini mai hawa biyu da ya ruguje a Kubwa, dake babban birnin tarayyar Abuja.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 11:25:25 na yammacin ranar Alhamis, kuma shaidun gani da ido sun ce ya samo asali ne sakamakon sauya tsarin ginin.