By Abbas Yakubu Yaura
Hukumomin kasar Rasha sun ce mutane 5 ne suka mutu yayin da 21 suka jikkata sakamakon wani hatsarin motar bas a kudancin birnin Moscow da sanyin safiyar ranar Lahadi.
Hukumar binciken ababan hawa ta kasar Rasha tace hatsarin ya afku ne da misalin karfe 5:45 na safe a agogon kasar dai dai da a gogon GMT (02:45) a yankin Ryazan.
“Sakamakon hadarin mutane biyar sun mutu. 21 sun ji rauni,” in ji hukumar ta Telegram, ta kara da cewa biyu daga cikin wadanda suka jikkata masu matsakaitan shekaru ne, sannan ya ce raunin da aka samu yana da “nau’i daban-daban.”
Hukumar ta ce motar bas din ta taka wani ginshiki ne da ke gefen gadar jirgin kasa yayin da hatsarin ya afku.
Kazalika Hukumar tace hatsarin ya afku ne a wata babbar hanya kusa da kauyen Voslebovo mai tazarar kilomita 270 kudu da birnin Moscow.
Jimillar fasinjoji 49 ne a cikin motar a cewar hukumomi.
Sannan ‘yan sanda sun ce sun bude shari’ar laifuka kan keta dokokin hanya, AFP.
Comments 1