By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Osun ta yi alkawarin ci gaba da samar da ababen more rayuwa ga yankunan karkara a jihar domin dakile yin kaura zuwa birane.
Gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola, wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin jama’a, Olatunbosun Oyintiloye, ya bayyana haka a wani shiri da ofishin hulda da jama’a na jihar ya shirya a ranar Alhamis a Isinmi Olootu, al’ummar dake kan iyakar jihar Osun da jihar Kwara.
Sannan yace wannan gwamnati mai ci tana jan hankalin al’umma musamman mazauna karkara domin lalubo hanyoyin inganta ababen more rayuwa da suke da su.
Ya kara da cewa , “Gwamnatinmu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sanya murmushi a fuskokin jama’armu na yankunan karkara saboda suna daga cikin muhimman abubuwan dake kawo nasarar gwamnatinmu.
“Wannan al’ummar tana kan iyakar Osun da jihar Kwara amma duk da haka, gwamnati na daukar kanta don ta zo ta duba bukatunku. Alamun cewa Oyetola yana da kyau kuma yana kula da duk mazauna yankunan daidai
“Yayin da muke mai da hankali kan ci gaban birane, ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen bunkasa yankunan karkara, haka ma don hana tafiye-tafiye daga karkara zuwa birane.”