An kashe Mutane shida a wani mummunan hatsari daya faru a Bauchi a ranar Litinin, wanda ya rutsa da Motocin haya guda biyu.
Kwamandan Shiyya na Hukumar kiyaye haɗurra ta Ƙasa dake Jahar Bauchi Yusuf Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin.
A cewar sa, mutane 19 sun samu raunuka a lamarin, wanda ya faru a ƙauyen Durum dake kan hanyar Bauchi zuwa Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Akalla Mutane 6 Ne Suka Mutu, 19 Suka Jikkata A Wani Hatsarin Mota A Jihar Bauchi
Lamarin na zuwa ne kwanaki huɗu bayan an kashe mutane 5, tare da jikkata wasu mutane 3 a mummunan hatsarin daya faru a ƙauyen Gubi dake kan hanyar Bauchi zuwa Kano.
Abdullahi yace a lokacin da aka kira su, sai da jami’an Hukumar suka ɗauki mintuna 20 kafin suje wajen lamarin domin ceto mutanen.
Yace an ɗauke duk wasu abubuwa akan hanyar, a yayinda aka miƙa abun hawan ga ofishin ƴan sanda.
Ya buƙaci Direbobi dasu guji tuƙin gaggawa, gami da bin dokokin tuƙi.