By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 19 suka jikkata a wani hatsarin mota daya afku a safiyar Laraba a kewayen unguwar Badeku dake Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Hadarin wanda ya rutsa da wata babbar mota mai lambar OYO: NRK 312 YR, da misalin karfe 7:00 na safe a mahadar Badeku dake kan titin Ibadan-Ile-Ife.
An tattaro cewa motar wadda take dauke da ma’aikata da dama, na kan hanyar ta zuwa Ikire da sauri, sai wata motar data fito daga kauyen Badeku, ta tsallaka titin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Majiyoyi sun bayyana cewa yunkurin da direban motar ya yi na kaucewa karo da ita ya sa ta yi taho-mu-gama, tare da fasinjojin da ke cikin motar.
Rundunar hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) da suka isa wurin da hatsarin ya afku, sun taimaka wajen kai wadanda lamarin ya rutsa dasu zuwa asibitocin dake yankin.
Da yake tabbatar da afkuwar hatsarin, kwamandan sashin FRSC na Oyo, Unce Chukwurah ya bayyana cewa motar tana dauke da leburori 26 a kan hanyarta ta zuwa wani wurin aikin gini.
“Hatsarin dai wanda ya rutsa da Motar tipper mai launin rawaya tana dauke da mutane 26, wanda 19 daga cikinsu sun jikkata, yayin da bakwai suka mutu a hatsarin.
“An kai wadanda suka jikkata an kaisu zuwa Asibitin ASBON da ke unguwar Gbagi domin yi musu magani, yayin da sauran ‘yan uwansu suka tattara gawarwakin mutane bakwai don binne su,” in ji shi.