By Abbas Yakubu Yaura
Bayan tattaunawa mai tsanani da aka yi tun da sanyin safiyar ranar Litinin, Majalisar Zartarwa ta kasa NEC, ta kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta kada kuri’ar fara yajin aikin gargadi na wata daya domin gwamnati ta amsa bukatunta.
A cewar wata majiya daga kungiyar, ta shaidawa Jaridar Vanguard cewa suna da kwarin Gwiwar cewa wannan yajin aiki na gargadi zai jawo hankalin Gwamnatin tarayya wajen biyan bukatun kungiyar.
“Muna son baiwa gwamnati doguwar igiya muna fatan za ta ga bukatar kauce wa gurgunta ayyukan ilimi a jami’o’in kasar nan.
Sannan kungiyar tace mu ma iyaye ne kuma muna da ‘ya’yanmu a cikin tsarin amma ba za mu iya kallo da kuma barin gaba daya tabarbarewar ilimi a kasar ba.
“Tashin hankalinmu yana da amfani ga kowa da kowa kuma idan tsarin ya inganta, duk za mu ji daɗinsa. Wasu fitattun mutane a kasar sun shiga cikin lamarin amma da alama gwamnati ta jajirce. Shugabanmu na kasa zai yi karin bayani ga manema labarai a yau,” inji shi.
Idan zaku iya tuna cewa kungiyar ta koka kan wasu bukatu da suka hada da biyan kudaden alawus din da aka samu na ilimi, asusun farfado da tattalin arziki, sauya tsarin biyan albashin ma’aikata na IPPIS, da tsarin fayyace ma’auni na jami’a UTAS, da dai sauransu.