By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane 4 ne suka mutu sakamakon hatsarin wani karamin jirgin sama daya fada ruwa dake birnin Brisbane na kasar Australia kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana a yau Lahadi.
‘Yan sandan jihar Queensland sun ce mutane hudun sun mutu ne bayan da karamin jirgin ya fado a gabar tekun kusa da Redcliffe, wani yanki na bayside a arewacin birnin, bayan karfe 9:00 na safe agogon kasar.
Acikin wata sanarwa da ‘yan sanda suka fitar tace “Ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto tare da jami’an ‘yan sandan ruwa na Queensland da masu ruwa da tsaki tare da sashin binciken hatsarin dake taimakawa wasu hukumomi, ciki har da Ofishin Tsaron Sufuri na Australia, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.”
Kwamishiniyar ‘yan sandan Queensland Katarina Carroll ta fadawa kafafen yada labaran cikin gida cewa martanin farko jirgin ya gamu da kalubalen rashin kawun yanayi.
Tace “Jirgin yana cikin wani yanayi mai matukar wahala, (a) matsayi mai wahala a yankin dausayi, kuma a halin yanzu muna da ‘yan sanda da masu ruwa da tsaki da ke tafiya zuwa wannan yanki, kuma abin da zan iya fada kenan a wannan matakin,” in ji ta.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya tabbatar da cewa mutane hudun ne kawai a cikin jirgin a lokacin da jirgin ya fado.