Isra’ila, wacce ke fama da mummunan harin da aka kai a yankinta cikin rabin karni, ta shelanta yaki a hukumance a kan kungiyar Hamas a ranar Lahadin da ta gabata yayin da adadin wadanda suka mutu a rikicin ya haura 1,000 bayan da kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta kai wani gagarumin farmaki daga Gaza.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ja kunnen al’ummar kasar da ke cikin firgici da alhini da su kwantar da hankalinsu.
Wasu Jamusawa da dama wadanda kuma ‘yan kasar Isra’ila ne, na daga cikin wadanda mayakan kungiyar Hamas ta Falasdinu suka yi garkuwa da su a lokacin farmakin da take kai wa Isra’ila, kamar yadda majiyoyin ministocin Jamus suka sanar a jiya Lahadi.
Karanta nanMun Rasa Mutum 200 Ta Sanadiyar Harin Sojojin Hamas Na Kasar Falasdinu-Kasar Isra’ila
Shugaban Amurka Joe Biden, duk da haka, ya ba da umarnin “ƙarin tallafi” ga Isra’ila bayan harin, fadar White House ta fada jiya Lahadi, ba tare da bayar da cikakken bayani ba.
Shugaban ya ba da umarnin ƙarin goyon baya ga Isra’ila dangane da wannan harin ta’addancin da Hamas ta kai wanda ba a taɓa ganin irinsa ba in ji Fadar White House a cikin wata sanarwa.
Rikicin da ya barke a Gabas ta Tsakiya ya kuma kashe mutane sama da 600 a bangaren Isra’ila, hasarar mafi muni da kasar ta fuskanta tun bayan yakin Larabawa da Isra’ila a shekara ta 1973 lokacin da ta fuskanci hari daga kawancen kasashen Larabawa karkashin jagorancin Masar da Siriya.
A Gaza da Isra’ila ta kai hare-hare kan wurare 800, gabanin abin da mutane da yawa ke fargabar cewa za a iya kaiwa hari, jami’ai sun ba da rahoton mutuwar akalla mutane 370, tare da jikkata wasu dubbai a fadin yankin da ake yaki.
Dubun dubatar sojojin Isra’ila ne aka jibge domin fafatawa da mayakan Hamas a kudancin kasar, inda aka tsinci gawarwakin fararen hula a jibge a kan tituna da kuma tsakiyar gari.
A wani labarin kumaDalilin da ya sa shirye-shiryen kawar da talauci yake faɗuwa – Robinson Uwak
Har yanzu abokan gaba suna nan a kasa,” in ji kakakin rundunar Daniel Hagari ga manema labarai yayin da dare na biyu ya fado bayan harin, ya kara da cewa Isra’ila na karfafa karfin soji a kusa da zirin Gaza.
An gwabza fada da bindigogi a lokacin da sojojin Isra’ila ke kokarin tabbatar da yankunan hamadar da ke kusa da gabar teku, da kubutar da Isra’ilawa da aka yi garkuwa da su tare da kwashe dukkan yankunan da ke kusa da Gaza.