Akalla mutane hudu ne suka mutu a ranar Lahadin da ta gabata yayin da wasu 14 suka samu raunuka a wani hadarin mota da ya rutsa da motar bas ta Mazda da wata babbar mota a Lufwape da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Ogun, Ahmed Umar ne ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Abeokuta ranar Lahadi.
Umar ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:40 na rana kuma direban motar ne ya haddasa shi.
Ya kara da cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce gona da iri da kuma tukin ganganci da direban motar ya yi.
A cewarsa, mutane 20 ne hatsarin ya rutsa da su da suka hada da maza 12 da mata takwas, yayin da maza takwas da mata shida suka samu raunuka yayin da maza biyu da mace biyu suka mutu a hatsarin.
Ya ce an kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin Idera da ke Sagamu domin yi musu magani, yayin da aka ajiye wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa na asibitin.
Umar ya gargadi masu ababen hawa kan illar tukin ganganci, inda ya ce, rayuwa ba ta da kwafi.
Ya shawarci jama’a masu tuka ababen hawa da su rika tuka mota na cikin kulawa, da kiyaye gudu tare da bin ka’idojin zirga-zirga.