Hukumar yaki da cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya, NCDC, ta ce mutum mutum 534 ne suka warke daga cutar kawo yanzu.
A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter a daren Alhamis, NCDC ta ƙara da cewa cutar ta korona ta kama 3145 baki daya ya zuwa daren. Sannan ta kashe mutum 103 kawo yanzu a fadin Nijeriya.