Wani hatsarin mota da ya auku da safiyar Lahadi a daidai Setraco Junction a babban titin zuwa Kubwa ya kashe mutum biyar tare da jikkata 8. Inda nan take aka garzaya da mutum takwas din asibitin. A cewar wani jami’in kiyaye hadurra ta kasa wato FRSC, Emmanuel Agbo, ya ce hatsarin ya auku ne a yayin da wata mota kirar Toyota Camry ta fito daga Kubwa zuwa cikin garin Abuja inda Tirela ta yi ciki da su. Agbo ya ce motar mai lamba ABC 978 SL, na dauke da Fasinjoji shida ne, inda ya tabbatar da cewa nan take mutum biyar ciki harda ma’aurata suka mutu. Yayin da mutum guda wace take mace ce ta tsira da ranta amma da raunuka. Ya tabbatar da cewa wadanda suka samu rauni, an kai su asibiti, yayin da wadanda suka mutu za a kai gawawwakinsu mutuware. Sannan ya ce bayan Tirelar ta buge su, ba ta tsaya ba, amma jami’an ‘yan Sanda sun bi ta sun kama ta. Wani jami’in dan sanda, Insfekta Danjuma Garba, ya tabbatar da kamun direban. Ya ce bayan hadarin ya auku, sun sanar da ‘yan sandan dake yankin, inda aka kama shi a daidai AYA.