Mutum daya ya jikkata inda kusan shaguna 50 suka kone a ranar Talata yayin da gobara ta tashi a kasuwar Bodija dake karamar hukumar Ibadan ta Arewa a Oyo,Tribune Online ta rawaito.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Har yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar da ta fara a yammacin ranar Talata ba yayin da gobarar ta cinye wani sashe na kasuwar katako.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Mummunar Gobara Ta Tashi a Wata Babbar Kasuwa a Jihar Oyo
Yayin da aka ce an kashe gobarar ne da hadin gwiwar jami’an kashe gobara na gwamnatin tarayya da na jiha.
Da yake bayyana irin halin da ya shiga, wanda lamarin ya rutsa da shi, Ahmed Abdulwasiu yana jinya a asibitin Calvary Baptist dake Bodija, Ibadan.
Abdulwasiu ya ce yana kokarin kashe gobarar da ta tashi a shagonsa ne kafin wutar ta kama shi, inda ya ce da ba don gaggawar shiga tsakani da mutanen da suka kawo masa dauki ba da tuni ya rasa ransa.
“Ina kokarin zuba ruwa ne domin tsayar da gobarar a rufin, kafin na shiga shagon, sai kawai na ga wutar ban sani ba cewa gobarar ta riga ta shiga ciki, rufin ya fado min, sai na makale a cikin shagon, babu wata hanyar tsira a gare ni, ina ta birgima kawai wuta ta biyo ni kafin mutane su zo ceto.”
Wani da abin ya shafa mai suna Mutiu Olaoluwa wanda ke da kayan daki ya ce, “Ina wajen shagona sai na ji tashin gobarar, kafin in ankara sai gobarar ta bazu zuwa shaguna biyu, gobarar ta fara bazuwa, wutar ta kone ko’ina”Kada ku fitar da komai, sama da kofofi 75 na abokin cinikina sun kone, katako na kusan na Naira N120,000 ya kone”.
“Na yi asarar sama da Naira miliyan 5 a gobarar saboda duk kayana, janareta, da injina sun kone, duk abin da nake yi a shekaru 30 zuwa 40 da suka gabata ya kone,” inji shi.
A wani labarin kuma, APC Ta Dakatar Da Wani Kwamishina Mai Ci
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Cross River a ranar Laraba ta dakatar da kwamishinan al’adu da yawon bude ido na jihar Mista Ekpenyong Iso.
An dakatar da Iso ne bisa zargin cin amanar jam’iyya da kuma karkatar da kudade.