By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa mutum daya ya mutu a wani hatsarin da ya afku a kusa da ofishin hukumar kula da hanyoyin mota da ababen hawa da ke unguwar Katampe a babban birnin tarayya Abuja a ranar Larabar da ta gabata.
Akalla mutane shida ne aka rawaito sun jikkata a hatsarin.
Daga cikin shidan da suka jikkata, an ce biyun suna cikin mawuyacin hali kuma suna karbar magani a asibitin kasa da ke Abuja.
Direban wanda aka ce yana kan matsanancin gudu sosai, ya samu matsalar birki ne yayin da hatsarin ya afku.
Wani ganau ya ce, “Tayyar gaban motar ta fashe ne yayin da direban ke cikin tsananin gudu. Ya yi kokarin taka birki amma abin ya faskara. Daga baya motar ta kutsa cikin magudanar ruwa a yankin. Dukkanin mutanen da ke cikin motar sun samu munanan raunuka kuma suna cikin mawuyacin hali.”
Kakakin hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa, Kalu Emetu, ya tabbatar da faruwar hatsarin.
Emetu ya ce, “Hatsarin ne shi kadai amma mutane da aka sanyawa motar sun yi yawa. Mutane bakwai ne a cikin motar; hudu a baya sai mutum uku harda direban suka zauna a gaba.
“Daya daga baya ya mutu a cikin ukun da aka kwantar a babban asibitin Mataima yayin da a cikin hudun da aka kwantar a asibitin kasa, biyu suna cikin koshin lafiya yayin da sauran biyun suka samu munanan raunuka.”