Rahotanni na nuna cewa mutum an kashe Mutum guda har lahira, yayin da wasu uku suka samu mummunan raunuka, sakamakon rikicin da aka yi na hana kungiyar dake ayyukan ci gaban Al’umma CDA gudanar da aiyukan ta a yankin Ubiaza da ke karamar hukumar Ikpoba Okha ta jihar Edo.
Mukaddashin kungiyar Odionwere na yankin, Pa Joe Osaheni ne ya bayyana wa hakan ga manema labarai a jiya Litinin a Benin, babban birnin jihar, inda ya ce, matsala ta Sami asaline daga ne lokacin da wasu mutane ke gudanar da ayyukan kungiyar CDA suka fara ayyukan su, duk da haramta ayyukan kungiyar da sarkin Benin, Ewuare II ya yi.
Kazalika ya Kuma zargi wani Mutum Mai suna Osabuohen Osagiede Uhunmwangho da haddasa rikicin, wanda kuma rikicin yayi sanadiyyar asarar dukiyoyi na miliyoyin nairori a yankin.
Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su shiga tsakani al’uma a yankin, don dakile karin asarar rayuka a yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nigeria na samun rahoton Cizon Macizai 20,000 a kowace shekara
Da yake mayar da martani, Osagiede Uhunmwangho ya musanta zargin, yana mai cewa, shi ba ya daya daga cikin al’umma yankin, kuma baya zama a wurin.
“Ba ni da masaniya kan abin da suke magana. Suna so kawai su bata mun suna, ”inji shi.
A nashi jawabin Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, DSP Kontongs Bello, ya ce haryanzu ba a yi masa bayanin kan abun da ya faru a yankin ba.
A wani labarin Kuma na daban.
Rundunar yan sanda a jihar Ekiti ta ce, ta kama mutane uku da ake zargin suna da hannu a garkuwa da wasu ma’aurata.
An yi garkuwa da mutanen ne a hanyar Ilasa zuwa Ayebode, da ke karamar hukumar Ekiti ta Gabas, da yammacin jiya Lahadi.
Rahotanni sun nuna cewa, Ma’auratan na dawo wa ne daga Ado Ekiti, inda suka je siyan kayayyaki a shirye -shiryen daurin auren su.
Daga baya masu garkuwa da mutanen sun tuntubi danginsu, inda suka nemi Naira Milliyan 5 a matsayin kudin fansa
Kakakin rundunar yan sandan jihar, ASP Sunday Abutu ya tabbatar da cafke mutane ukun da ake zargi da hannu a garkuwa da Ma’auratan.
Comments 1