Mutumin da masu garkuwa da mutane suka harba a lokacin da suka ɗauke iyalansa a jihar Kaduna ya rasu.
’Yan bindiga sun tare Omega da ’yan uwansa a hanyarsu ta zuwa gona inda suka yi awon gaba da mutane 17 daga cikinsu a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
“Ya rasu da misalin ƙarfe 3.00 na asuba a Birnin-Gwari inda ake jinyarsa, kafin a dawo da shi Udawa aka binne shi da misalin ƙarfe 10 na safe”, inji kawunsa, Malam Umaru.
Baya ga mamacin wanda ’yan bindigar suka harba a baki, sai mata biyu ’yan uwansa da suka samu munanan raunuka a harin suna kwance a asibiti a Birnin-Gwari.
Ya ce dole ta sa aka mayar da marasa lafiyar asibitin daga inda aka fara kai su a Kaduna saboda iyalan ba za su iya biyan kudin asibiti ba.
Har yanzu babu labarin ’yan uwansu 17 da aka yi garkuwa da su, waɗanda a cikinsu har ada mace mai shayarwa.