Jami’an gwamnatin Saliyo sun bayyana cewa kusan fursunoni 2,000 ne suka tsere a harin da aka kai a barikin soji da gidan yari da sauran wurare a kasar ranar Lahadi.
Mukaddashin Darakta Janar na Hukumar Kula da Gidan Yari ta Saliyo, Kanar Shek Suleiman Masakui, ya ce an kai harin na sa’o’i biyu.
Karanta nanKiristoci A Jahar Bauchi Sun Yaba Wa Gwamna Bala Akan Mutunta ‘Yancin Addini
A cewar wani rahoto da jami’an gidan yarin suka rabawa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Litinin, wasu fursunoni 1,890 ne suka tsere daga gidan yarin na Pademba bayan da maharan suka kutsa kai.
Idan dai za a iya tunawa, maharan sun jefa kasar da ke yammacin Afirka cikin firgici da sanyin sa’o’i bayan da aka yi ta harbe-harbe a babban birnin kasar, Freetown.
Gwamnati ta zargi sojojin da suka yi tawaye da ta ce an fatattake su.
Rundunar ‘yan sandan, a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, ta bukaci fursunonin da su koma gidan yari, tare da bai wa jama’a tukuicin samun cikakken bayani kan inda wadanda suka tsere ko kuma maharan suke.
A wani labarin kumaGwamnati Ta Ware Biliyan 3.23 Don Sanya Na’urar Gano Bam A Filayen Jiragen Nijeriya
A halin da ake ciki gwamnatin Amurka da kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka sun yi Allah wadai da wannan karyar da sojojin suka yi.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, ofishin jakadancin Amurka da ke Saliyo ya nuna rashin amincewarsa da fasa gidan yarin yayin da ya bukaci hadin gwiwa da jami’an tsaron gwamnati.
Amurka ta ce ta tabbatar da goyon bayanta ga zaman lafiya, dimokuradiyya, da wadatar kasar Saliyo.