Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya yaba da hukuncin kotun daukaka kara da ta tabbatar da zaben sa.
A wata sanarwa da sakataren yada labaran Aliyu, Malam Abubakar Bawa ya fitar, gwamnan ya ce hukuncin ya zama shaida ga bangaren shari’a na Najeriya.
Karanta nanMutun 1,800 Suka Tsere Daga Gidan Kurkuku-Gwamnatin Kasar Saliyo
Aliyu ya danganta wannan nasara da yardar Allah Ta’ala,inda ya kara da cewar muna kallon wannan nasara a matsayin albarkar Ubangiji, kuma muna yaba wa bangaren shari’a don tabbatar da gaskiya da adalci,” in ji Aliyu.
Ya bukaci ‘yan adawa da su ba shi hadin kai domin tabbatar da ci gaban jihar Sokoto,Gwamna ya tabbatar wa al’umma yadda gwamnatin sa ta himmatu wajen samar da ribar dimokradiyya.
Muna ci gaba da jajircewa wajen samar da yanayi mai kyau ga ci gaba a jiharmu,alkawarinmu na kokarin da ake yi na kawar da ‘yan bindiga da masu aikata laifuka ta hanyar ci gaba da aiyukan soji in ji Aliyu, inda ya nemi goyon bayan masu ruwa da tsaki.
Aliyu ya bukaci ci gaba da bayar da goyon baya daga jama’a, yana mai jaddada bukatar hadin kai wajen ganin an samu sauyi a jihar.
A wani labarin kumaYau Kotu Za Ta Yanke Hukunci Akan Zaben Gwamnan Jahar Ribas
Ya nuna jin dadinsa da goyon baya da addu’o’i da jama’a suka ba su, inda ya yaba da rawar da suke takawa a cikin nasarorin da jihar ta samu tare da karfafa gwiwar karin addu’o’i, shawarwari da kuma sukar ci gaban jihar.
NAN ta ruwaito cewa kotun daukaka kara ta Abuja ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke na zaben gwamna a ranar Litinin, inda ta tabbatar da nasarar Aliyu a zaben 2023.
Jam’iyyar PDP a jihar, ba ta gamsu da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamna ta yanke, ta daukaka kara zuwa kotun daukaka kara.