By Abbas Yakubu Yaura
Wani mamba a tawagar masu aikin ceto ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, zaftarewar kasa a wata mahakar ma’adanai dake Jadawa a arewacin kasar Myanmar a jiya ta kashe akalla mutum daya, tare da raunata 25, da kuma bata wasu da dama.
Da yawan jama’a suna mutuwa a kowace shekara na masu aiki a cikin kasuwancin ja da ake samun riba amma mara kyau, wanda ke amfani da ma’aikata bakin haure masu karancin albashi don kawar da wani dutse mai daraja a makwabciyar kasar Sin.
Bala’in dai ya afku ne a wata mahakar ma’adinai dake garin Hpakant kusa da kan iyaka da kasar Sin a jihar Kachin, inda ake kyautata zaton ana tono biliyoyin daloli na ma’adinan mai daraja daga tsaunukan yankin a duk shekara.
“Kimanin mutane 70 zuwa 100 ne suka bace” biyo bayan zaftarewar kasa data afku da misalin karfe 4:00 na safe (21:30 agogon GMT a ranar Talata), in ji wani mamban tawagar ceto Ko Nyi.” Mun aika da mutane 25 da suka jikkata zuwa asibiti yayin da muka samu macacce daya. ”
“Suna hako ma’adinan da daddare kuma da safe sai su fitar da kasa su wanke shi” in ji mai fafutukar, ya kara da cewa karin nauyi ya sa kasar ta rufta cikin ramin.
Ya kara da cewa, kimanin masu aikin ceto 200 ne ke aikin gano gawarwakin inda wasu ke amfani da kwale-kwale wajen neman wadanda suka mutu a wani tafkin da ke kusa da wajen
Sojoji sun hana shiga mahakar ma’adinan da ke arewacin kasar, kuma hanyoyin sadarwar intanet basu da yawa a yankin.