By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina tace ta kama wani mutum mai suna Sani Mamuda mai shekaru 45 da haihuwa bisa zarginsa da bayar da makamai da alburusai ga ‘yan bindiga a jihohin Katsina da Zamfara.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isa, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin a ranar Alhamis a hedikwatar ‘yan sanda dake Katsina.
A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne da safiyar ranar Laraba a kan hanyarsa ta zuwa Zamfara domin kai bindigu kirar AK-47 guda biyu da magazine guda biyu dauke da harsashi 42 na harsashi mai girman 7.62 mm.
Isa ya kuma bayyana cewa wanda ake zargin ya boye makaman ne a karkashin kujerar babur din daya hau a jihar Zamfara.
“A ranar 22 ga watan Disamba, 2021, da misalin karfe 7:30 na dare, bisa ga sahihan bayanan sirri, DPO Kurfi da tawagarsa sun kama Mamuda a karamar hukumar Birnin Magaji ta jihar Zamfara.
“Mamuda, wanda ya kasance fitaccen dan fashi da makami ne, wanda ya kware wajen samar da makamai ga ‘yan bindiga a dazuzzukan jihohin Katsina da Zamfara, an kama shi ne a hanyar Kurfi-Batsari a kan hanyarsa ta daga jihar Katsina zuwa jihar Zamfara.
“Sauran abubuwan da ake zargin an samu awajen Mamuda sun hada da CFR 12,000; na Naira 49,500; wayar Techno daya da layukan Airtel guda biyu.
“Mamuda ya amsa cewa ya sayi bindigu guda biyu a dajin Mashi daga hannun Masa’idu daya kuma da wajen Abdullahi wadanda a yanzu suke hannun su,” inji Isa.
Kakakin ‘yan sandan ya ce tuni aka fara gudanar da bincike a kan wanda ake zargin, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun data dace bayan kammala shi.
Wanda ake zargin a lokacin da yake amsa tambayoyi, ya amsa cewa yana kai makaman ne ga wasu ‘yan bindiga a jihar Zamfara.
Mamuda yace yana samun riba tsakanin Naira 50,000 zuwa Naira 80,000 kan kowace bindiga daya sayar.
Ya kara da cewa, “Burin samun biyan bukata ya sa na shiga wannan sana’ar kimanin shekaru biyu da suka wuce. Ina ba da makamai ne kawai ga ‘yan fashi. Ban taba kashe mutane da wadannan makamai ba.”