Wata mata da ke Kano ta auri saurayin diyarta bayan ganin diyar ta ki amincewa da soyayyarsa, Legit.ng ta ruwaito.
Sabuwar amaryar ta kashe aurenta ne bayan ganin wani saurayi ya nemi auren diyarta ta ki amincewa.
Wannan yasa ta nemi sani daga malamai kafin ta dauki mataki kuma suka tabbatar mata da cewa abinda ta yi ba haramun bane.
Duk da dai ‘yan uwanta ba su yi na’am da lamarin ba amma haka nan ta yi auren. Kamar yadda Daily Trust ta bayyana, lamarin ya auku ne a karamar hukumar Rano da ke Kano kuma sunan diyar matar Aisha, wacce ta ki amincewa da auren mutumin.
Matar mai suna Malama Khadija ta yanke wannan shawarar ne don kada duk su taru su yi asara kuma itama ta ga tana da kyau kamar diyarta.
Ta bayyana cewa sai da ta nemi sani daga malamai sannan ta dauki matakin ba kara zube kawai ta yi hakan ba, sannan ta tuntubi ‘yan uwan mijinta.
A kalamanta:
“Ban yi hakan bisa jahilci ba. Sai da na nemi sani daga malamai inda suka ce ba haramun bane. Yayin da na tuntube shi sai ta amince, amma iyaye da ‘yan uwana sun ki yarda da auren.
“Wannan ne dalilin ne ya sanya na garzaya wurin Hisbah inda suka yi mana aure.”
Ta bayyana cewa ta matsa wa mijinta ne har sai da ya sake ta duk da iyaye da ‘yan uwanta sun ki amincewa da hakan.
Matar Aure Ta Kashe Aurenta Tayi Wuff Da Saurayin Ɗiyarta
Malama Khadija tace ta yanke shawarar ta auri mijin nata na yanzu ne bayan ɗiyar ta tace bata son sa.
Majiyar mu ta shafin Linda Ikeji ta samo cewa a wata hira da gidan rediyon Freedom, Malama Khadija tace da sauran lafiyarta sannan tana zaune cikin kwanciyar hankali da mijinta na yanzu.