An samu wata cakwakiya a ƙaramar hukumar Rano ta jihar Kano, bayan wata mata mai suna, Malama Khadija, ta kashe aurenta ta auri saurayin ƴar ta.
Malama Khadija tace ta yanke shawarar ta auri mijin nata na yanzu ne bayan ɗiyar ta tace bata son sa.
Majiyar mu ta shafin Linda Ikeji ta samo cewa a wata hira da gidan rediyon Freedom, Malama Khadija tace da sauran lafiyarta sannan tana zaune cikin kwanciyar hankali da mijinta na yanzu.
KU KARANTA KUMA: Messi na shirin watsawa PSG ƙasa a ido, akwai yiwuwar ya koma Barcelona
Ta yi bayanin cewa bayan ta fahimci ɗiyarta ta ƙi amsar soyayyar sa, sai taji cewa bai kamata su duka suyi asarar sa ba, hakan ya sanya ta nemi iyayen sa, inda ta ƙara da cewa itama kyakkyawa ce kamar ɗiyarta.
“Ban yi hakan cikin jahilci ba. Na tuntuɓi malamai inda suka gayamin ba haramun bane. Lokacin da na gaya masa aniya ta, bai yi musu ba, amma iyayena da ƴan’uwana sun ƙi yarda suyi min wakilci kan auren. Hakan ya sanya na garzaya wajen Hisbah inda yanzu gashi muna zaune lafiya.” A cewar ta.
Da yake magana dangane da lamarin, wani kawun Khadija, Abdullahi Musa Rano, yace sun hanata ta aure shi ne saboda da gangan ta kashe aurenta domin ta auri saurayin ɗiyarta. Sannan gabaɗaya ahalin su ba suyi maraba da wanann auren ba.
“Ta takurawa mijinta sai ya saketa domin ta auri mutumin. Ba zamu yi wannan abin kunyar ba a ahalin mu hakan ya sanya muka ƙi aurar da su. Ba muji daɗin abinda Hisbah tayi ba kuma zamu kai ƙorafi domin mu dawo ƴar mu. Muna neman babbar rundunar Hisbah ta jiha da gwamnatin jiha da su sanya baki kan wannan lamarin.”
Ko da aka tuntuɓi kwamandan Hisbah na yankin, Ustaz Sani Rano, sai ya kada baki yace rundunar Hisbah ta jiha ce kaɗai ke da hurumin yin magana akan lamarin.
Ƴan Sanda Sun Cafke Wani Tsoho Bisa Bayar Da Cin Hancin N1.5m Domin a Saki Ɗan Ta’adda
A wani labarin na daban kuma, ƴan sanda sun cafke wani tsoho bisa bayar da cin hancin maƙudan kuɗaɗe domin a saki ɗan ta’adda.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta cafke wani mutum mai suna Bamuwa Umaru, shekara 62 a duniya, bisa laifin bayar da cin hancin N1m domin a sako wani mai garkuwa da mutane.