Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya nemi daukin gaggawa daga hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA kan tallafawa ‘yan gudun hijira dubu dari takwas da suke da bukatuwa ga abinci a yankunan da ta’addanci a jihar ya yiwa raga-raga.
Hakan ya fito ne a sanarwar da Malam Isa Gusau, mai taimakawa gwamnan kan harkokin watsa labarai ya fitar a ranar Juma’a.
Inda ya ce gwamnan ya nemi hakan ne a takardar da ya rubutawa NEMA a yayin da ya kai musu ziyara a hedikwatarsu dake birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis, inda ya shaidawa shugaban NEMA din ‘yan gudun hijirar na cikin matsanancin halin neman gudummawa a garuruwa 11.
Zulum ya shaidawa Daraktan NEMA, AVM Muhammadu Alhaji Mohammed (mai ritaya) cewa; ‘yan gudun hijirar na zaune ne a Monguno, Bama, Damboa, Gwoza, Dikwa, Gamboru, Ngala, Damasak, Banki, Pulka da Gajiram.