Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta kashe sama da dala biliyan 1 wajen sayen kayan aikin soji domin kwato yankunan Arewa maso Gabas da Boko Haram ta kama. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Femi Adesina, mai ba Buhari shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a ne ya bayyana hakan a ranar Talata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon Shugaban APC da Daruruwan Magoya Bayan Jam’iyyar Sun Sauya Sheka Zuwa PDP
A cewar sanarwar, taron zaman lafiya na Abu Dhabi ne ya karrama Buhari da lambar yabo don karfafa zaman lafiya a Afirka.
A cikin jawabinsa a taron zaman lafiya na Afirka 2023 a Mauritania, Buhari ya bayyana cewa Afirka da sauran kasashen duniya suna aiki tukuru don magance barazanar wanzuwar bil’adama.
“Lokacin da na zama shugaban kasa a shekarar 2015, Boko Haram sun rike kusan kashi biyu bisa uku na jihar Borno, rabin jihar Yobe, da kuma wasu kananan hukumomi biyu a jihar Adamawa, duk a Arewa maso Gabashin Najeriya.
“Mun sami damar maido da wadannan yankuna ta hanyar zuba jari fiye da dala biliyan 1 don samun makamai masu karfi da manhajoji daga Amurka da sauran kasashen da muke abokantaka da su don gudanar da ayyukan ci gaba da yaki da ta’addanci tun 2015.”
A wani labari kuma, Ka Bar Real Madrid Ba Ma Bukatar Ka –Guti Ya Fada wa Modric Ya Bayyana Wanda Zai Maye Kurbinsa
Tsohon shahararren dan wasan Real Madrid Guti Hernandez ya bayyana wa dan wasan tsakiyar Kungiyar Luka Modric cewa, ba a bukatarsa kungiyar.
Ya kara da cewa, Dan wasan na Croatia ya kamata ya kuduri aniyar karkare wasannin shi a Babban kungiyar ta Kasar Sifaniya saboda matashin dan wasan Borussia Dortmund Jude Bellingham na shirin maye gurbinsa.