Kyaftin din Argentina Lionel Messi ya ce ya san zai lashe kofin duniya.
Da yake magana bayan da ya zaburar da Argentina ta lashe kofin duniya na farko cikin shekaru 36 a ranar Lahadi, Messi ya ce: “Na san cewa Allah zai ba ni nasarar lashe kofin, na ji cewa wannan nawa ne.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kasar Argentina Ta Lashe Kofin Duniya, Bayan Doke Faransa
“Ba za mu iya jira mu kasance a Argentina don ganin yadda bikin zai kasance ba.”
“Wannan shi ne kofin da nake so a rayuwata. Wannan shi ne burina tun ina karami.”
“Shi ne mafi kyawun abin da akwai [Kwafin Duniya]. Kalli yadda yayi kyau.”
“Ba zan yi ritaya daga kungiyata ta kasa ba. Ina so in ci gaba da taka leda a matsayin zakara.”
Messi ya zura kwallaye biyu a wasan karshe da suka buga da Faransa da ci 3-3 mai kayatarwa. Ya mayar da bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda kungiyar ta ci 4-2.
A wani labarin kuma, ‘Yan Najeriya 300 Sun Isa Kasar Jordan Domin Gudanar Da Aikin Hajjin 2022
Kimanin ‘yan Najeriya 300 ne suka isa birnin Amman, babban birnin kasar Jordan lami lafiya domin gudanar da aikin hajjin bana na shekarar 2022 a kasa mai tsarki.
Maziyartan sun isa birnin Amman ne da sanyin safiyar ranar 17 ga watan Disamba domin gudanar da aikin hajji na kwanaki 9 a wuraren tarihi na koyarwar Yesu Almasihu kamar yadda aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki na Bible.
Gwamnan Enugu, Mista Ifeanyi Ugwuanyi ne ya dauki nauyin mahajjatan zuwa kasa mai tsarki.
A ranar farko ta ziyarar, mahajjatan sun gudanar da kewaye a wurin tarihi na Katadel wanda ke kan wani tudu a yankin Amman.