Daga Mukhtar Yakubu Kano
Jaruma Amal Umar, wacce tana daya daga cikin jarumai mata da masana’antar fina-finai ta Kannywood ta ke ji da su a wannan lokacin, ta bayyana cewar, in dai ana maganar tarbiyya to ita a gidan tarbiyya ta taso, domin gidan su gidan tarbiyya ne.
Jarumar ta yi wannan Kalaman ne a lokacin da take amsa tambayar wakilin jaridar Dimokuradiyya, dangane da irin kallon da a ke yi wa jaruman fim musamman mata na rashin kamun kai, da kuma rashin tarbiyya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yadda wata Yar Nigeria ta yi aikin Leburanci kafin saurayin ta ya Bata Naira 2,000
Inda take cewa, “Ni dai abin da za iya cewa, ko a fim din Hausa ana zargin mu ana ce mana ‘yan iska ne mu, wanda kuma mutane su na manta wa da cewa, tarbiyya fa tarbiyya ce, duk yadda ka taso a gidan ku a haka za ka rika rayuwa ko da ka fito waje. To ni dai na taso a gidan tarbiyya ne, kuma ko da na ke wannan fim din, ban fuskanci kalubale ba, saboda duk inda na je, ina tuna wa da cewar ni Musulma ce, kuma Bahaushya ce” a cewar ta.
Comments 1