Na yarda cewa zaben 25 ga watan Fabrairu bai yi daidai ba – Shugaban APC, Adamu
Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya amince cewa zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu bai yi dai-dai ba, domin akwai kura-kurai.
Adamu ya yi wannan jawabi ne a yammacin ranar Litinin a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a taron kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na kasa tare da Bola Tinubu, zababben shugaban kasa, Kashim Shettima, mataimakin shugaban kasa, da kuma zababbun ‘yan majalisar wakilai ta kasa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ban sayi gidaje ba ko na saci kudin gwamnati na kaisu Dubai ba – El-Rufai
Taron na sirri wanda aka fara da misalin karfe 2:50 na rana, an gudanar da shi ne a dakin taro na Banquet House dake Abuja.
Da yake jawabi a wajen taron, Adamu ya kuma taya daukacin zababbun jiga-jigan siyasa murna, inda ya jaddada cewa sun cancanci yin farin ciki da nasara bayan lashe zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Adamu ya ce, “Ina matukar taya daukacin manyan mutane maza da mata da aka zaba. Ina gaisheku baki daya. Ku ne sabuwar tawagar Najeriya. Daga ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekara, nauyin hadin kan kasarmu, zaman lafiya, da ci gabanmu zai rataya a wuyanku a matsayin kungiya.
“Yana da kyau da daraja a yarda cewa zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu bai cika ba. Ba mu shirya gudanar da cikakken zabe ba.
“Tarihi na duniya ba shi da wani yanayi na cikakken zaɓe. Kamar sauran al’ummomin dimokuradiyya, mun himmatu wajen gudanar da zabubbuka masu inganci da gaskiya. Wannan mun yi.
“Daga sakamakon zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, babban zaben da hukumar zabe ta INEC ta sanar zuwa yanzu, jam’iyyar APC ce ta lashe zaben shugaban kasa, da tsafta, kuma mafi rinjaye a majalisun tarayya biyu.
A wani labarin kuma:Yadda Uba ya yi wa ɗiyar sa mai shekaru 18 fyade a shagon sa
Wata Kotun Majistare da ke Ikeja da ke zama a Ogba, Jihar Legas, ta tasa keyar wani mutum mai shekaru 36, Roland Okajere, a gidan yari na Kirikiri bisa zargin yi wa ‘yarsa ‘yar shekara 18 fyade a cikin shagonsa da ke yankin Ikotun a jihar.
Alkalin kotun, Mista L. A Owolabi ya ba da umarnin ne bayan da aka gurfanar da wanda ake tuhuma wanda ke fuskantar tuhuma kan laifin fyade da ‘yan sanda suka gano a kansa a ranar Litinin.