Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC), ta ja hankalin jama’a kan yawaitar magungunan ganye na (Herbal) da ba a amince da su ba a fadin kasar.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Kayayyakin magungunan wadanda ta bayyana a matsayin “masu hadari”.
KARANTA WANNAN NAFDAC Ta Fasa Kamfanin Sarrafa Maganin Baban Aisha
Babbar darakta na Hukumar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta shaida wa manema labarai a Abuja ranar Litinin din nan cewa, galibin magungunan da ake amfani da su na ganye ne na snuff da na liquid, wadanda ta ce barayi ne a tituna ke siyar da su.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa Babban daraktan ya kuma lura cewa, tawagar rundunar hukumar sun fara aikin dakile masana’antun da ‘yan kasuwar da ke siyar da irin wadannan kayayyakin da ba a tantance ba.
A Wani Labarin Kuma Babbar Sallah: Sarkin Musulmi A Nigeria Ya Bayyana Ranar
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ayyana ranar Laraba 28 ga watan Yuni a matsayin ranar 10 ga watan Zul-Hijjah na shekarar 1444 bayan hijira a Najeriya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Majalisar Sarkin Musulmin Alhaji Sa’idu Maccido ya fitar ranar Litinin din nan a Sokoto.
“Alhaji Sa’ad Abubakar, Shugaban Majalisar Koli ta harkokin addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ya ayyana ranar Litinin 19 ga watan Yuni a matsayin ranar 1 ga watan Zul-Hijjah 1444H.
“Don haka, Laraba, 28 ga watan Yuni, wanda zai yi daidai da 10 ga Zul-Hijjah za a yi bikin Eid-el-Kabir wato babbar Sallah na shekarar 2023,” in ji shi.
Ya yi wa al’ummar Musulmi fatan alheri da neman shiriyar Allah.
Yadda Sifen Ta Lashe Kofin Kasashen Turai
Tawagar kwallon kafa ta kasar Sifen ta samu nasarar lashe kofin kasashen Turai bayan nasarar da ta samu akan abokiyar karawarta Kurotiya
Sifen wadda ta lashe kofi a karon farko cikin shekaru 11 ta buga mintuna 90 ba tare da zura kwallo a ragar Kurotiya ba abinda yasa Alkalin wasa ya bushe wasan kuma ya kara mintuna 30 domin cigaba da fafatawa.
Daga karshe dai aka tashi wasan babu ci wanda yasa aka tafi bugun daga kai sai mai tsaron raga
Dan wasan Real Madrid Dani Carvajal ne ya zura kwallo ta karshe kuma wadda ta zama dalilin lashe kofin da kasarsa tayi.