Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta ce ta karbi samfurin wasu magungunan Covid19 guda biyu, domin Tantance su.
Jami’in Hulda jama’a da jama’a na hukumar Mr Olusayo Akintola ne ya bayyana hakan a a wata Sanarwa da aka rabawa manema labarai a yau Lahadi.
Kazalika ya kuma Musanta rade radin da ake cewa hukumar ta karbi wani kalar Ganyan shayi, domin Tantance shi a matsayin maganin Covid19.
Anta bangaren Shugabar hukumar NAFDAC din, Moji Adeyeye ta ce a koda yaushe sukan mayar da hankali ga abubuwan da al’umma ke bukata.
A cewar ta yanzu haka yanzu haka an baiwa kwararru damar ga gudanar da kan magungunan domin gano irin illar su, kuma da zarar sun kammala bincike za a ji Sanarwa ta gaba.