Dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya gargadi magoya bayansa da su guji sukar abokan takararsa.
Obi ya yi wannan gargadin ne a yau Lahadi ta shafin sa na Twitter.
Da yake nuna damuwarsa kan wannan lamari, Obi ya ce ya gane cewa wasu daga cikin magoya bayansa suna ta zage-zage da kai hare-hare kan wasu masu neman takara da ’yan takara.
Obi, wanda ya gode wa magoya bayansa kan goyon bayan da suka ba su, ya bukace su da su, da su ci gaba da marawa kowa baya cikin mutunta.
Ya yi nuni da cewa, ya kamata a gudanar da zabe a dimokuradiyya, yana mai cewa goyon bayan masu neman takara baya bukatar haifar da makiya.
Tsohon gwamnan Anambra ya ce, “An jawo hankalinsa, ya kuma lura cewa wasu da yawa daga cikin magoya bayansa suna kai hare-hare kan wasu masu neman takara.