Tauraruwar fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta sanar da cewa daga yanzu ba za ta ci gaba da fitowa a shirin nan mai dogon zango ‘Labarina’
Tauraruwar ta tabbatar da haka ne a saƙon da ta wallafa a shafinta na Intagram ranar Asabar da daddare.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da ɗuminsa: Kachalla, Auta, da wasu manyan Kwamandojin ƴan bindiga sun baƙunci Lahira a Zamfara
Ta ce ta ji daɗin rawar da ta taka a cikin shirin, sai dai ta ce ba za ta iya ci gaba da shi ba saboda wasu dalilai na ƙashin kanta.
Sai dai kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito, wasu majiyoyi sun bayyana cewa ta ɗauki matakin ne saboda rashin jituwar da aka samu tsakaninta da mai shirya shirin kuma shugaban kamfanin Saira Movies, Malam Aminu Saira.
Nafisa ita ce babbar tauraruwa a shirin na Labarina da ya samu karbuwa matuƙa a wurin ƴan kallo, inda ta fito a matsayin Sumayya.