Daga: Abbas Yakubu Yaura
Ministan matasa da ci gaban wasanni Mista Sunday Dare, ya ce Najeriya ce ma fi kyawun ‘yan wasa masu tuka keke a nahiyar Afirka.
Dare ya bayyana haka ne a lokacin da shugaban kungiyar CAC Mohammed Azzam da shugaban kungiyar CFN Giandomenico Massari suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa da ke Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/majalisar-dokokin-anambra-ta-amince-da-sake-fasalin-kudurin-kasafin-kudin-2022-na-naira-biliyan-169-6/
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa a ranar Alhamis (yau) ne ake sa ran za a fara gasar tseren keke ta nahiyar Afirka na shekarar 2022 a Abuja wanda kuma za’a kammala a ranar Lahadi.
Ministan ya ce yana fatan Najeriya ta samu damar ciyo lambobin yabo a gasar.
Ya roki shugaban CFN da ya ci gaba da bunkasa harkar wasanni a Najeriya, domin ya samu damar mamaye nahiyar.
“Muna so mu gode wa CAC saboda goyon bayan da take baiwa masu tseren tuka keke na Najeriya, don su kasance cikin mafi kyawu a duniya.
“Muna fatan ‘yan wasan Najeriya za su ci gaba da samun irin wannan tallafin,” in ji shi.
Shugaban CFN, Giandomenico Massari, ya godewa ministan bisa baiwa hukumar damar karbar bakuncin taron na nahiyar.
Ya ce taron zai baiwa ‘yan Najeriya masu tuka keke da takwarorinsu na wasu kasashen Afirka damar baje kolin fasaharsu.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta ta rawaito cewa Najeriya ta lashe gasar zakarun nahiyar karo na farko a Abuja a shekarar 2019.
Jimillar kasashe 15 ne za su halarci gasar tseren tuka kekunan.
NAN