…Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce har yanzh Najetiya ba ta iya cimma alkawarin da aka kulla ba kan ware kaso a fannin kiyon lafiya.
Hukumar lafiya ta duniya (WHO), ta ce har yanzu Najeriya ba ta iya cimma matsaya ba a shekarar 2001 da kashi 15 cikin 100 na sanarwar Abuja kan inganta fannin kiwon lafiya.
Dr Walter Mulombo, Wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a Najeriya ya bayyana haka a Abuja a wata ganawa da manema labarai.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta ruwaito cewa, a cikin watan Afrilun 2001, shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Afirka sun yi taro inda suka yi alkawarin ware akalla kashi 15 cikin 100 na kasafin kudinsu na shekara don inganta fannin kiwon lafiya.
KU KARANTA KUMA WHO Ta Shirya Bunkasa Lafiyar Mutane Biliyan 3 A 2023
“A Najeriya inda aka tsara cewa kashi 15 na kasafin kudin gwamnati ya kamata ya kasance a fannin lafiya, har yau ba mu cimma burinmu ba,” in ji shi.
Mulombo ya ba da shawarar karin kudade na fannin kiwon lafiya don cimma burin da aka sa a gaba, yana mai cewa bangaren ba a samun isassun kudade, idan aka kwatanta da bangarori kamar na tsaro, da sojoji da sauransu.
A cewarsa, lafiya hakki ne na dan Adam ba kamar kayan alatu ko abin amfani ba, idan aka kara zage damtse cikin hikimar siyasa a kasar nan za ta amfanar da wannan al’umma.
“Muna buƙatar fara magana game da take haƙƙin ɗan adam saboda ba a yarda da kowane yaro ya rasa maganin rigakafi ba,” in ji shi.
Ya ce wasu wuraren da kungiyar ta shiga sun nuna cewa kashi 80 na kudaden basa shiga manyan asibitoci.
A cewarsa, fannin kiwon lafiya na farko shi ne inda kashi 80 cikin 100 na al’ummar yankuna ke samun bayyanarsu ta farko ga ayyukan kiwon lafiya. (NAN)
A Wani Labarin Kuma Tsoffin Kansilolin Arewacin Najeriya Sun Amince Da Sanatan Kano Ya Shugabanci Majalisar Dattawa Ta 10
Kungiyar tsofaffin kansilolin Arewacin Najeriya ta amince da Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Barau Jibrin a matsayin wanda zai shugabanci majalisar dattawa ta 10.
Taron dai ya amince da goyon bayan tsayawa takarar Sanata Jibrin na jagorantar majalisa ta 10 a matsayin shugaba kuma shugaban majalisar dattawa, duba da irin dimbin gogewar da yake da ita a majalisar.