Wani matashi mai suna @1issa_m, ya burgw mutane sosai kan yadda bai ɗorawa kansa ƙarya ba.
Matashin ya sanya bidiyon sa a TikTok inda ya nuna ɗakinsa ɗaya tal wanda ba a daɗe da kammala ginin sa ba, jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Jami’an tsaro sun ceto matar wani babban basarake da ƴan bindiga suka sace
Ya bayyana cewa ina alfahari da nasarar da ya samu duk kuwa da cewa wasu za suyi tunanin cewa ɗakin nasa yayi ɗan ƙarami da yawa.
Yayi nuni da cewa har yanzu yana da sauran lokaci sannan wata rana ta iya yiwuwa ya samu ƙatoton gidan da zai yi tutiya da shi, ta yadda mutane za su yi maganganun su, su gama.
Mutane sun yaba masa sosai kan wannan namijin ƙokarin da yayi inda suka bashi tabbacin cewa wannan ɗaki ɗayan da ya gina babbar nasara ce.
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda Dimokuraɗiyya ta tattaro:
@Mashembu ya rubuta:
“Wannan shine ake kira gida.”
@Cyndie ya rubuta:
“Kayi ƙoƙari. Bulo guda nawa kayi amfani da shi.”
@xolisambobo ya rubuta:
“Kayi ƙoƙari, wannan gagarumin cigaba ne kake samu.”
@akon8561 ya rubuta:
“Kayi ƙoƙari ɗan’uwa, damuwata shine kalar bulon M6 a wajen yin fandisho. Yanayin barandar ka ta iya baka matsala lokacin iska.”
Ku kalli bidiyon a nan
“Sai Kace Uwa Da Ɗa” Hotunan Wata Shirgegiyar Mata Da Mijinta Sun Girgiza Intanet
A wani labarin na daban kuma, mutane sun cika da mamaki bayan bayyanar bidiyon wata shirgegiyar mata da ɗan siririn mijinta.
Wata mata ƴar duma-duma ƴar Najeriya mai suna, Mimi Christabel, ta garzaya soshiyal midiya inda ta nuna mijinta yayin da take duba kan irin rayuwar gwagwarmayar da suka sha a baya tare.
Mimi ta sanya wani tsohon hoto da ta ɗauka tare da mijinta, inda take nuni da cewa soyayyar su tun ta yarinta ce.