Tsohon gwamnan jihar Sokoto, kuma mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya nuna damuwarsa a ranar Lahadi kan ‘yan fashin da ke addabar yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
Bafarawa ya ce hakan na haifar da babbar barazana ga samar da abinci a Najeriya.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Bar Jihar Legas Zuwa Birnin Tarayya Abuja
A maimakon maganar nade-naden ministoci, tallafi, da tattalin arziki, kamata ya yi gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta dauki batun samar da abinci a matsayin fifiko.
Dattijon ya kuma yi gargadin cewa idan ba a dauki tsauraran matakai na dakile tashe-tashen hankula ba, Arewa za ta fuskanci koma-baya mai tsanani na ilimi nan da shekaru 50 masu zuwa.
Bafarawa, wanda ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da jaridar PUNCH, ya ce an rufe makarantun firamare da sakandare da dama a Arewacin Najeriya saboda ayyukan ‘yan bindiga, yana mai cewa, “Wannan babban bala’i ne.”
Wakilinmu ya rawaito cewa, yayin da sanarwar da gwamnati ta fitar na cire tallafin man fetur ya kai ga karin farashin kayan abinci da kayan masarufi, tattaunawa kan nadin minista da shugaban kasa ya yi ya mamaye tattaunawa a ‘yan kwanakin nan.
Amma Bafarawa ya shawarci gwamnati ta tsara abubuwan da ta sa a gaba daidai.
Ya ce, “Maimakon maganar ministoci, tallafi, da tattalin arziki, kamata ya yi gwamnati ta yi la’akari da samar da abinci domin a halin da muke ciki, nan da watanni uku masu zuwa, tabbas za mu fuskanci matsaloli a Najeriya, musamman a Arewa maso Yamma.
“’Yan fashin sun ki barin manoma su yi noma. Wannan lamari dai yana da matukar hadari, ba wai kawai ‘yan fashin na kashe mutane ba, har ma da yadda matsalar karancin abinci za ta yi kamari a ‘yan watanni masu zuwa, musamman a yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
“Don haka muna son gwamnati ta farka ta yi wani abu a kai.
“Kazalika da yadda ilimi ke tafiya, nan da shekaru 50 masu zuwa, za mu koma baya a fannin ilimi, domin yawancin makarantun firamare a Arewa an rufe su ne saboda ‘yan fashi.
“Babu makarantun firamare, babu makarantun sakandare kuma wannan babban bala’i ne. Don haka, ba za mu iya zama mu duba ba; dole ne a yi wani abu daidai kafin ya yi muni.
“Ya kamata gwamnati ta yaki tsaro, musamman matsalar karancin abinci, a kasar, domin lamari ne mai tsanani. Duk abin da gwamnati za ta yi, a bar batun samar da abinci ya zama fifiko.”
A wani labarin kuma, Yawan Rai: Saudiyya Ta Kaddamar Da Taswirar Aikin Hajjin Badi
Ma’aikatar kula da Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya a ranar Juma’a a birnin Makkah ta kaddamar da taswirar aikin hajjin shekarar 2024 mai.zuwa.
Ministan aikin hajji da Umrah na Saudiyya Tawfiq Al Rabiah ne ya kaddamar da taswirar hanyar a wani biki da ya samu halartar shuwagabanni da wakilan alhazai a kasar.