Shugaban Ma’aikatan Hukumar kula da Tsaron Najeriya Manjo-Janar Lucky Irabor, ya bayyana cewa yaji kunya da takaici cewa Sojojin Najeriya basuyi hangen ƴan bindiga zasu kai hari a Makarantar Horas da Manyan Jami’an Soji ta Ƙasa dake Kaduna.
Ya bayyana haka a ranar Juma’a a lokacin da yayi jawabi a Shirin Urgent Conversation na Radio Now 95.3.
Irabor yace Makarantar NDA kamar kowacce Makaranta ce, to don haka Soji basu ga buƙatar bata wani laƙabi na musamman ba.

KARANTA WANNAN LABARIN: Zanga zangar adawa da zaben Iraqi ya rikiɗe zuwa Tarzoma
Yace “Makarantar horaswa ce da ake kira Nigeria Defence Academy ko kuma Makarantar Soji ba yana nufin ba ɗaya take ba da wata makaranta, duk da cewa naji kunya ace bamu ga faruwar irin wannan lamari ba.
Ƴan bindiga da suka kai hari a Makarantar a watan Ogusta sun kashe Sojoji biyu tare da sace wani Babban Soja mai Muƙamin Manjo. Wannan lamari ya haifar da damuwa a tsakanin ƴan Najeriya musamman ganin cewa soji nada alhakin kare ƙasar.
Amma Manjo-Janar Irabor ya musanta wannan damuwar, yana mai cewa Sojin Ƙasa koda yaushe suna akan kai hari, yana mai bayyana harin Makarantar Horas da Jami’an Soji na NDA a matsayin Fashi.
Irabor yace lamarin bai karya lagon Jami’an Soji ba, tunda suna da ƙarfin kare Ƙasar.
“Harin da aka kai a Makarantar NDA ba yana nufin cewa ba’a kai mana hari a kullum, ko kunsan yanayin harin da ake kai mana? Inji shi.