Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo a ranar Juma’a ya jinjinawa Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai bisa kammala aikin ruwan Zariya wanda aka kwashe sama da shekara 42 ba a yi irin wannan aikin ruwan ba a jihar.
Namadi Sambo ya yi wannan jinjinar ne a yayin da ya kai wa gwamnan ziyara a Kaduna. Rahotanni sun nuna cewa aikin ruwan Zariyar, tsohon mataimakin shugaban kasar ne ya fara a lokacin da yake gwamnan Kaduna.
Aikin ruwan Zariyar ana sa ran mutane miliyan biyu ne za su amfana da aikin. Inda Namadi Sambo ya ce; “wannan aikin abin jinjinawa ne.” in ji shi. Ya kara da cewa; gwamnan ya yi kokarin magance matsalar ruwan Zariya da aka dade ana fama da shi wanda zai bunkasa zamantakewa da tattalin arzikin jama’a.
Namadi Sambo ya ce ya ji dadin ambaton sunansa da aka yi a aikin ruwan Zariyan.