Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a ranar Talata ya jaddada kudirin gwamnati na ci gaba da hukunta wadanda ake zargin Mayakan Boko Haram.
Malami, yayin da yake karbar jakadan Najeriya a kasar Netherland, Eniola Ajayi, yace an fara shirin ci gaba da gudanar da shari’ar kotuna na musamman a Kainji da ke New Bussa na jihar Neja domin gurfanar da wasu da ake zargi da aikata ta’addanci.
AGF, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Umar Gwandu, ya fitar, ya ce: “Tare da bin umarnin Najeriya a karkashin doka ta 86 ta Rome Statute of ICC, Najeriya ta bayar da cikakken hadin kai ga kotun ta hanyar mika takardun da suka dace, da rahotannin kwamitin bincike da sauransu”.
Ya ce tuni aka kafa wani kwamiti cikin gida a Najeriya da ake kira da Rome Statue, domin gudanar da bincike.