Hukumar sadarwa ta kasa NCC na shirin samar da cibiyoyin sadarwa domin bayar da taimakon gaggawa a jihohi 36 na kasar nan, da kuma birnin tarayya Abuja.
Shugaban hukumar Farfesa Umar Garba Danbatta ne ya bayyana hakan a jihar Enugu ne ya bayyana hakan a jiya Asabar, yayin taron baje kolin da aka gudanar a jihar, wanda yanzu haka yake ci gaba gudana. Prime Time News ta rawaito.
KU KARANTA: Ukraine Tayi Tir Da Sabon Muƙamin Rasha A Kwamitin Tsaro na MDD
A cewarsa manufar samar da cibiyoyin shine cike gibin da ake samu a yankuna daban daban na kasar kan tsaikon samun taimakon gaggawa da ake da bukata daga hukumomin dake da alaqa da batun da ya taso.
Farfesa Dambatta wanda ya samu wakilcin daraktan hulda da jama’a na hukumar Mr Reuben Muoka, a yayin taron, yace ya zama wajibi kamfanonin sadarwa dake aiki a kasar nan, su samar da hanyar kira domin neman taimakon gaggawa kyauta zuwa ga muhimman bangarori ta hanyar amfani da lambobin nan guda na 112 a kowace jiha cikin jihohin kasar nan.
Sai dai ya shawarci duk masu amfani da yanar gizo da kada su bude wasikun imel da ba su saba da su ba, ya kara da cewa kada mutane su sanya bayanan sirri ta yanar gizo.
Muoka ya ce hukumar ta samar da lambar kira kyauta 622, a matsayin Mataki na biyu wanda ke baiwa masu amfani da su damar kara kaimi ga matsalolin da ba a warware su ba daga masu ba da sabis nasu ga hukumar don samun mafita mai inganci.
Shugaban ya bayyana sakonnin tes da ba a nema ba a matsayin wani babban al’amari da ke damun masu amfani da wayar, inda ya kara da cewa hukumar domin kare masu amfani da wayoyin daga wannan dabi’a ta rashin kyau ta samar da mafita mai suna.
A wani labarin kuma: Ku Shirya Barin Gidan Gwamnati – ADC ta Fadawa Gwamnan APC
Jam’iyyar ADC shiyyar Kudu maso Gabas, a ranar Asabar, ta shawarci Sanata Hope Uzodimma da jam’iyyar APC a jihar Imo da su fara tattara kayansu daga gidan gwamnatin jihar kafin ranar 11 ga watan Nuwambar 2023.
Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Kudu Maso Gabas, Kwamared Chilós Godsent ne ya bayar da wannan nasihar a madadin jam’iyyar yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron kwamitin ADC na shiyyar Kudu maso Gabas ZWC da aka gudanar a ranar Asabar a Owerri, jihar Imo domin duba zaben 2023.