A tsakiyar mamayar Ukraine, Rasha ta karbi shugabancin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na watan Afrilu, kamar yadda gidan talabijin na Al-Jazeera ya rawaito.
Wannan dai wani bangare ne na karba karbar shugabancin a tsakanin kasashe mambobi 15 na kwamitin sulhun Majalisar.
KU KARANTA: APC ta Maka INEC, NNPP A Kotu Kan Sakamakon Zaben Gwamnan Kano
Ana saka ran Rasha ba ta da wani tasiri kan yanke shawara amma ita ce za ta jagoranci manufofin kwamitin.
A cewar rahotannin Moscow ta karshe ce ta jagoranci majalisar a watan Fabrairun 2022, kuma a wannan watan ne ta mamaye Ukraine.
Mamayar dai lamarin da ya sa Kyiv ta yi kira da a cire Rasha daga majalisar.
Hukumomin Ukraine sun yi tir da wannan ci gaban, suna mai bayyana shugabancin Rasha na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a matsayin abun Allah Wadai.
Ta bakin ministan harkokin wajenta, Sergey Lavrov, Moscow ta ce tana shirin jagorantar wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a wannan watan kan tare da ministan ya jagoranci muhawara kan gabas ta tsakiya a ranar 25 ga Afrilu.
A wani labarin kuma: Ku Shirya Barin Gidan Gwamnati – ADC ta Fadawa Gwamnan APC
Jam’iyyar ADC shiyyar Kudu maso Gabas, a ranar Asabar, ta shawarci Sanata Hope Uzodimma da jam’iyyar APC a jihar Imo da su fara tattara kayansu daga gidan gwamnatin jihar kafin ranar 11 ga watan Nuwambar 2023.
Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Kudu Maso Gabas, Kwamared Chilós Godsent ne ya bayar da wannan nasihar a madadin jam’iyyar yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron kwamitin ADC na shiyyar Kudu maso Gabas ZWC da aka gudanar a ranar Asabar a Owerri, jihar Imo domin duba zaben 2023.