Rundunar hukumar hana sha da fataucin muggan ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta sanar da cewa ta dakarunta sun yi nasarar cafke sinadarin ephedrine da kuma nitrous oxide dake sa dariya.
Rundunar ta ce ta samu nasarar ce a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad dake Legas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kaduna Ta Kaddamar da Rukunin Gidajen Kwanan Dalibai 400
NDLEA ta ce tana kyautata zaton an yi safarar kayayyakin ne daga kasar Afirka ta Kudu da kuma Sudan.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta hannun kakakinta Femi Babafemi ta ce wasu da yan ƙungiyar fasa kwaurin muggan kwayoyi ta DTO ne suka shigo da kayayyakin inda tuni aka yi nasarar cafke su.
“Bisa rahotannin sirri da muka samu ne jamian mu na asiri suka samu nasarar kama wani mai suna Suleiman Babatunde Oba wanda ya shahara wajen safarar kwayoyi a kasashen Brazil da Mozambique da Ghana da kuma Agirka ta Kudu gami dq wasu yankuna nahiyar turai.”
“Mun kama shi ne lokacin da yake kokarin hawa jirgin Rwanda da ta nufi Afirka ta Kudu inda ya cusa kayayayykin acikin buhun gatin Semivuta.
NDLEA ta ce Suleiman na da Fasfon Afirka ta kudu inda kuma yake auren yar kasar bayan share shekaru ashirin yana zama a can.
Yanzu haka akwai wani ma’kacin tashar jirgin mai suna Godwin Shedrack da ake zarginsa da hannu wajen safarar muggan ƙwayoyi.