Ndume ya bada Miliyan 40 tallafi ga Manoma, Yan kasuwa da Ɗalibai
Dan majalisa mai wakiltar Yammacin Borno, Muhammad Ali Ndume ya bada Miliyan arba’in don tallafin sa ga Yan kasuwa, manoma da Ɗalibai.
Ndume ya bada taki cikin babbar mota guda goma, sannan da irin masara daban-daban cikin babbar mota uku, Don rarrabawa manoma dake Karamar hukuma tara, don farfado da noma a yankin.
KARANTA:-Yan majalisu sun amince da maida tara shigo da kayan fasa kwauri daga 1,000 zuwa 1,000,000
A yayin bikin kaddamar da raba tallafin, a garin Biu, Mataimakin gwamna Umar Usman Kadabur, ya yabawa Sanata kan irin gagarumar gudummawa da yake yima Mutanen yanki, da kuma kokarin sa na tallafawa mata da matasa don habakar tattalin arziqin su da dogaro da kansu.
Kadabur yace, irin wannan babbar gudummawa zata dade tana taimakawa Al’umma musamman cikin wannan yanayin rashin tsaro, hakan kuma zai bada damar samun aiki ga Mutanen.
Ya kuma shawarci wadanda suke da rabon samun tallafin da suyi amfani dashi ta hanyar data dace don cin moriyar sa.