By Ishaq Dabai
Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji, Ali Ndume, ya yi Allah wadai da kashe wasu jami’an soji a jihar Borno da wasu mahara suka yi a lokacin kwanton bauna.
Ndume, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a Abuja ranar Lahadi da daddare, yace abin da ya faru, duk da rashin sa’a, bai isa ya rage wa sojojin karfin iko ba.Ya kuma bukace su dasu ci gaba da yaki da masu tayar da kayar baya a kokarin kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan.
Sannan ya kara da cewa a matsayinta na kasa, dole ne ‘yan Najeriya su ci gaba da karfafa gwiwa tare da yi wa babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya fatan samun nasara a yakin da yake yaki da masu tayar da kayar baya.
Ndume, wanda kuma ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da kar tayi kasa a gwiwa wajen bayar da kudaden gudanar da ayyukan soji, yace, “kisan da aka yi wa sojoji tsakanin Marte da Dikwa a Jihar Borno abin Allah wadai ne.“Abin bakin ciki ne da rashin sa’a. Wannan bai kamata ya karaya sojoji daga kai wa masu tada kayar baya yaki ba.
Muna mika ta’aziyyar mu ga iyalan wadanda aka kashe tare da yin addu’ar Allah ya basu hutawa ta har abada musamman yadda suka mutu yayin hidimar kasarsu.
Sojoji da dama da ke kan hanyar wucewa kuma suna kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno, wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne dake da alaka da ISWAP sun yi musu kwanton bauna, inda suka kashe da dama daga cikinsu.